ABNA24 : Wannan dai na zuwa ne kwana uku bayan da shugaban kasar Donald Trump, ya kamu da cutar, wacce yake jinyarta a yanzu haka.
Mme McEnany, ta sanar da cewa bayan gwaje gwajen da take yi tun daga ranar Alhamis wadanda basu nuna tana dauke da cutar ba, yau sakamakon gwajin data yi ya nuna ta harbu da cutar.
Ta ce yanzu dai babu wasu alamu da take ji, saidai kuma ta killace kanta a yanzun.
Bayanai daga AMurka sun ce a yanzu haka dai muhawara ta kaure kan sakacin fadar White House da iyalen shugaba Trump, na daukar matakan kariya game da cutar ta korona.
Ko a ranar Lahadi kakakin fadar shugaban ta Amurka, ta gudanar da taron manema labarai ba tare da ta sanya takunkumin rufe baki da hanci ba.
A wani labari kuma daga Amurka, rahotonni sun ce mai yiwa a sallami shugaban Trump daga asibiti a wannan Litinin.
342/